2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

Gabannin zaben 2019, shugabannin kungiyar matasan Kudu sun amince da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake takara.

A wajen wani taro a Lagas, shugabannin matasan sun kuma nuna ammincewarsu da shugaban hafsan sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai da sauran shugabannin tsaro.

Kungiyar ta bayyana irin tarin nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a fannin tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa a matsayin dalilin tsayar da shi.

Kungiyar ta kuma yi watsi da tugun da wasu yan siyasa ke shiryawa kasar tare da tsorata mutanen kasar saboda son zuciyarsu game da zaben 2019.

2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

Sun kuma yabama rawar ganin da bangaren shari’a ke yi wajen hukunta wadanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

Sun kuma jinjinawa rundunar sojin Najeriya kan yadda akayi bikin karamar Sallah cikin kwanciyar hankali a fadin kasar musamman a yankin arewa maso gabas inda yan gudun hijra suka yi bukukuwan sallah a gidajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel