Olu Falae: SDP ya zuwa yanzu bata da dan takarar shugaban kasa a badi

Olu Falae: SDP ya zuwa yanzu bata da dan takarar shugaban kasa a badi

- Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya yace basu da tsayayyen Dan takara

- Ya tabbatar da cewa burin SDP shine su zabi dan takara mafi nagarta da zai kawo cigaba, hadin kai da daukakar kasar

- SDP ita ce jam'iyyar Abiola wadda ta lashe zaben 1993

Olu Falae: SDP ya zuwa yanzu bata da dan takarar shugaban kasa a badi

Olu Falae: SDP ya zuwa yanzu bata da dan takarar shugaban kasa a badi

Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya yace basu da tsayayyen Dan takara. Ya tabbatar da cewa burin SDP shine su zabi Dan takara mafi nagarta da zai kawo cigaba, hadin kai da daukakar kasar.

A takaitacciyar hira a murnar cika shekaru 80 ta Editan ofishin jakadancin labarai, farfesa Victor Olufemi Adefela, wanda aka yi a Legas, shugaban jam'iyyar SDP ya roki yan Najeriya da su fitar da jam'iyyar APC daga mulki a zabe mai zuwa kuma kada suyi tunanin dawo da tsohuwar jam'iyyar PDP mulki a 2019.

Kamar yanda yace, "Jam'iyyun biyu sunyi iya kokarin su, wanda bai haifarwa da kasar komai ba. PDP tayi shekara 16 ba tare da wani cigaba ga kasar nan ba kuma APC tayi shekara 3 itama ba wani canji a kasar."

Tsohon shugaban jam'iyyar SDP din ya hori yan Najeriya dasu zabi SDP wacce yace tafi kowacce jam'iyyar samu cigaba a kasar nan.

DUBA WANNAN: Mayatar video games ka iya zaras da matasa, inji WHO

Kamar yadda yace, "Saboda dalilai masu yawa da yan Najeriya suka sani, suna ta tururuwar komawa jam'iyyar SDP domin tunkarar zaben 2019 mai zuwa. Bazamu ba yan kasar kunya ba kuma munyi alkawarin zamu fitar wa da yan Najeriya da Dan takara mafi cancanta a matakin tarayya, jiha da karamar hukuma."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel