Hutun sallah da aka je ya kwashe N100b daga kasuwannin hannun jari

Hutun sallah da aka je ya kwashe N100b daga kasuwannin hannun jari

- Shi dai hutu yana kassare harkar kasuwancin saboda ba kamar kasuwar gari ake hada-hada a Stock Exchange ba

- Kasuwa ce da ake aiki litinin zuwa juma'a, kuma ana yinta ne da zamani

- HAnnayen jari kan hau su adi, dai dai da yanayin kasuwa

Hutun sallah da aka je ya kwashe N100b daga kasuwannin hannun jari

Hutun sallah da aka je ya kwashe N100b daga kasuwannin hannun jari

Kasuwannin saka hannayen jari da hada-hadar masarufi ta Najeriya, watau Nigerian Stock Exchange, dake Legas, tayi faduwar warwas inda masu jari suka rasa uwar kudi har N96b a hutun kwana biyu na juma'a da litinin da aka tafi.

Shi dai hutu yana kassare harkar kasuwancin saboda ba kamar kasuwar gari ake hada-hada a Stock Exchange ba.

Kasuwa ce da ake aiki litinin zuwa juma'a, kuma ana yinta ne da zamani.

Ya zuwa yanzu dai, Tiriliyan ta naira har tara ce ake hada-hadar da ita, saboda masu zuba jarin sun aje kudadensu da yawa.

DUBA WANNAN: Har yanzu SDP bata da dan takara

Daga fannin arewacin Najeriya dai, babu yan kasuwa sosai da suke zuba jari a wannan kasuwa ta zamani, kuma babu iilimin fahimtar yadda ake hada-hadar, su dai, har yanzu, irin kasuwancin kaka da kakanni suka sani, wal bani wal baka, wal keke da keke.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel