Shugaba Buhari ya bayyana adadin kudin ayyukan da 'yan majalisa suka cusa a kasafin kudin 2018

Shugaba Buhari ya bayyana adadin kudin ayyukan da 'yan majalisa suka cusa a kasafin kudin 2018

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya yayin da yake sa hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018 a fadar gwamnatin sa a bayyana cewa 'yan majalisar tarayya sun yi masa jagwalgwalo akan kasafin kudin da sunan dubawa.

Shigaban kasar dai ya bayyana cewa 'yan majalisar sun rage kudaden ayyukan sa da suka kai akalla sama da Naira biliyan 300 akan ayyuka sama da dubu 4 da ya kuduri aniyar yi.

Shugaba Buhari ya bayyana adadin kudin ayyukan da 'yan majalisa suka cusa a kasafin kudin 2018

Shugaba Buhari ya bayyana adadin kudin ayyukan da 'yan majalisa suka cusa a kasafin kudin 2018

KU KARANTA: Naga jiya da shekaranjiya, Buhari na yau ba zai tada mun hankali ba - Obasanjo

Legit.ng ta samu cewa haka zalika shugaban yace 'yan majalisar sun kuma cusa ayyukan su sama da dubu 5 akan kudi Naira biliyan 578 na kashin kan su wanda kwata-kwata hakan bai masa dadi ba.

A wani labarin kuma, Haramtattun kaya na akalla sama da Naira biliyan 1.3 ne jami'an rundunar hukumar kwastam ta kasa suka kama tun daga tsakiyar watan jiya ya zuwa farkon wannan watan da muke ciki na Yuni kamar dai yadda kwanturolan shiyya ta 'A' Mohammed Uba ya shaidawa majiyar mu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel