Kungiyar CAN ta nesanta kanta daga goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari

Kungiyar CAN ta nesanta kanta daga goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari

Kungiyar CAN ta nesanta kanta daga goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari

Kungiyar Kiristoci a Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN mai suna Samson Ayokunle ya nesanta kungiyar sa da wani rahoto da suka ce yana yawo na cewa suna goyon bayan takarar tazarcen shugaba Buhari a zaben 2019.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Fasto Adebayo Olajide, mataimakin sa na musamman akan harkokin watsa labarai da ya ce su kungiyar su ba ta siyasa bace.

Kungiyar CAN ta nesanta kanta daga goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari

Kungiyar CAN ta nesanta kanta daga goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari
Source: UGC

KU KARANTA: Wasu 'yan madigo sun shiga matsala a Kano

Legit.ng ta samu cewa da yake karin haske game da batun, Fasto Adebayo ya ce wasu ne masu kungiya mai sunan ‘Change Advocates of Nigeria (CAN) da ke da lakani iri daya da tasu kungiyar ne suka ce hakan amma ba su ba.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi fa na kowane dan Najeriya ne mai irin kowane addini, yare ko kabila ciki kuwa hadda Tijjaniyya tare da cewa shi babban burin sa shine na samar wa da 'yan kasa cigaba mai dorewa.

Shugaban yayi wannan ikirarin ne a fadar sa dake a Villa, jiya lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin darikar Tijjaniya a nahiyar Afrika karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass dake zaman jika wurin Marigayi Sheikh Ibrahim Inyass.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel