Manyyan ayyuka na 5 da majalisar tarayya suka ragewa kudi a kasafin kudin 2018 - Buhari

Manyyan ayyuka na 5 da majalisar tarayya suka ragewa kudi a kasafin kudin 2018 - Buhari

A jiya ne dai shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rattafa hannu akan kasafin kudin shekarar 2018 biyo bayan gama yin 'yan gyare-gyare da majalisar tarayya tayi a kan sa kamar dai yadda dokar kasa ta tanada.

Sai dai lamarin ya zo da 'yar hatsaniya bayan da shigaban kasar ya zargi 'yan majalisar da lalata masa lissafi musamman ma wajen yadda suka shigo da wasu bakin bukatun su a ciki sannan kuma suka rage masa nashi.

Manyyan ayyuka na 5 da majalisar tarayya suka ragewa kudi a kasafin kudin 2018 - Buhari

Manyyan ayyuka na 5 da majalisar tarayya suka ragewa kudi a kasafin kudin 2018 - Buhari

KU KARANTA: Buhari zai rabawa 'yan Najeriya kudin da Abacha ya sata

Legit.ng ta samu cewa shugaban kasar ya lissafa da yawa daga cikin manyan ayyukan da ya kuduri niyyar yi a shekarar ta 2018 amma 'yan majalisar suka zaftare masu kudade.

Ga dai wasu daga cikin su nan:

1. Wani bangare na kudin da gwamnati ya kamata ta zuba a cikin ayyukan tashar wutar Mambilla, gadar Niger ta biyu da ma hanyar Legas zuwa Ibadan.

2. Wasu manyyan ayyuka a cikin garin Abuja da suka hada hadda na aikin sufurin jirgin kasa.

3. Aikin kara tsaurara tsaro a hedikwatar majalisar dinkin duniya dake a garin Abuja.

4. Wasu manyan ayyuka a makarantun gaba da Sakandare da samar da magunguna a sibitoci

5. Karin tsaro a makarantun musaya guda 104 na gwamnatin tarayya a dukkan fadin kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel