An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

- Sama da jam'iyyun siyasa 100 ne zasu shiga zaben 2019

- Ya zuwa yanzu mutane miliyan 9m ne aka ƙara yiwa rijistar katin zabe

- Nan da wani lokaci ƴan Najeriya dake ƙasashen waje zasu fara zaɓe daga can inda suke

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta koka kan yadda ake ƙara samun yawaitar jam'iyyun siyasa a ƙasar, domin kuwa a cewarta jam'iyyu kusan 100 ne zasu shiga zaɓen shekara mai zuwa 2019.

An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

Domin kuwa ƙungiyoyin siyasa 138 ne suke neman hukumar tayi musu rijista don zama cikakkiyar jami'yya.

Da yake magana a yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Abuja Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS) ta tura jami'anta wuraren yin rijistar zaɓen a ƙasa baki ɗaya, kuma har ma sun cafke mutane 300 bisa yunƙurin yin rijistar.

KU KARANTA: Da yiwuwar shugaba Buhari zai gana da ‘yan sabuwar PDP - Fadar shugaban kasa

Shugaban na INEC ya kuma shaida cewar ya zuwa ranar 24 ga watan Mayu, kimanin mutane miliyan tara ne aka sake yiwa rijista domin su samu damar kaɗa kuri'arsu a zabe mai zuwa, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da hukumar ta yiwa rijistar zuwa kusan miliyan 80m.

Farfesan Yakubu ya kara da cewa hukumar zaɓen tana nan ta duƙufa wajen tsara wani daftarin dokar da zai bawa ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar yin zaɓe. Haka zalika INEC ɗin na aiki tare da hukumomin tsaro domin magance siyen ƙuri'a yayin zaɓe. Kamar yadda Farfesan ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel