Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

- Sojin saman Najeriya sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane

- An ceto mutanen ne a ranar Laraba 20 ga watan Yunin 2018

- Kamar yadda sojin ta bayyana, anyi nasarar ceto mutanen ne saboda bayyanan sirri da aka samu kuma aka tabbatar dashi da jirgi mai na'urar leken asiri

Sojin saman Najeriya ta ce jami'an ta rundunar gagawa na QRG da ke Gusau sunyi nasarar ceto mutane uku da masu garkuwa da mutane suka tsare na tsawon makonni uku a karamar hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara.

Kakakin hukumar Sojin saman, AVM Olatokunbo Adesanya ne ya bayar da wannan sanarwan a ranar Laraba 20 ga watan Yuni a Abuja.

Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

Ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne bayan wasu jami'an sojin na musamman sun kai simame ta sama da kasa a sansanin yan barandan da ke Dajin Kagara a karamar hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara.

"Wata runduna ta musamman ne sojin saman ne suka ceto mutanen bayan samun bayanan sirri daga mazauna garin sannan hukumar sojin tayi amfani da jirgi mai leken asiri ta tabbatar da inda yan barandan ke buya.

"Anyi amfani da sabon jirgi mai saukan angulu kirar EC - 135 sannan wasu sojojin na musamman suka kai simame ta kasa yayin da ake kai harin," inji shi.

A cewar Adesanya, sojin saman za su cigaba da kai wasu hare-haren a cikin makonni masu zuwa don tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Hukumar Sojin Saman ta samar da jirgin yaki mai saukan angulu kirar EC-135 ga dakarun sojin da ke aikin samar da tsaro a jihar Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel