Gardawa 4 sun Lakada ma Mijin yar uwarsu duka har lahira, sakamakon cutarta da yake yi

Gardawa 4 sun Lakada ma Mijin yar uwarsu duka har lahira, sakamakon cutarta da yake yi

Hankula sun tashi a unguwar Ifira Akoko dake cikin karamar hukumar Akoko ta kudu na jihar Edo, inda a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni wasu gabza gabzan matasa suka lakada ma minin yar uwarsu duka har sai da yace ga garinku nan, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutumin, Adelogba Ademuyiwa mai shekaru 45 a rayuwa ya sha dukan ajali ne a hannun matasan su hudu sakamakon zarginsa da suke yi da cin zarafin yar uwarsu da yake aure, mai suna Itunu.

KU KARANTA: Kafa da kafa: Buhari zai kai ziyarar jaje Bauchi bisa ibtila’in da ta fada ma al’ummar jihar

Mazauna unguwar sun bayyana cewa Matasan sun jibgi Adelogba ne don rama ma yar uwarsu irin duka da cin mutuncin da take sha a hannunsa, wanda suke ganin abin ya ishesu. Wani makwabcin Adelogba Ademuyiwa yace:

“Ya saba dukanta, kulla muna gani yake dukanta, a ranar Talata ne yayi mata dukan kawo wuka da har sai da aka garzaya da ita zuwa Asibiti, inda a wannan karon yan uwanta sun gaji da irin wannan cin mutunci, ba tare da wata wata ba wasu matasa suke iske shi a Asibitin, inda suka caccasa shi har sai da ya mutu.” Inji shi.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar Edo, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni jami’an Yansanda sun bazama farautar matasan nan guda hudu, zuwa yanzu har sun damko wuyar guda daga ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel