Kafa da kafa: Buhari zai kai ziyarar jaje Bauchi bisa ibtila’in da ta fada ma al’ummar jihar

Kafa da kafa: Buhari zai kai ziyarar jaje Bauchi bisa ibtila’in da ta fada ma al’ummar jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirye shiryen kai ziyara jihar Bauchi don jajanta musu kan ibtila’in da ta fada ma jihar a cikin yan kwanakinan, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

Wata gobara ne ta tashi a babbar kasuwa garin Azare, wanda ta kona komai kurmus, wanda hakan ya janyo mamakon asara da yan kasuwar suka tafka, haka nan anyi iska da ruwa masu karfi da suka yi sanadin mutuwar wasu da jikkata wasu, duka biyu a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a cikin barikin Sojojin Najeriya

Da fari dai shugaba Buhari ya aika da wata tawaga a karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu zuwa jihar Bauchi don jajanta ma al’ummar jihar bisa wannan ibtilai, sai dai a yanzu ya canza shawara, don kuwa an ce zuwa da kai ya fi sako.

Babban mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da mutuwar mutane takwas tare da jikkatar mutanr dari da ashirin a sanadiyar iska da ruwa mai karfi da aka kwashe sama da awa daya ana yi, haka zalika yace gidaje 1,505 sun lalace.

Bugu da kari, Garba Shehu yace kimanin shaguna dari takwas ne suka kone kurmus a babban kasuwar garin Azare dake karamar hukumar Katagum.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel