Kasar Amurka ta tiso keyar ‘yan Najeriya 34 gida, akwai dalili

Kasar Amurka ta tiso keyar ‘yan Najeriya 34 gida, akwai dalili

A kalla mutane 34 ‘yan asalin Najeriya kasar Amurka ta dawo da su gida a yau, Laraba, 20 ga watan Yuni, 2018.

Wadanda aka dawo da su din sun sauka a sashen saukar jiragen daukan kaya na filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas da misalign karfe 2:30 na rana.

Daga cikinn mutanen akwai 32 maza da mata 3, kuma dukkan su an dawo das u ne a cikin wani jirgin sama na kamfanin Omni International aircraft mai lambar rijista W342AX.

Kasar Amurka ta tiso keyar ‘yan Najeriya 34 gida, akwai dalili

Kasar Amurka ta tiso keyar ‘yan Najeriya 34 gida

Da yake Magana da kamfanin dillancin labarai na kasa, kakakin filin jirgin sama na jihar Legas, Joseph Alabi, ya tabbatar da isowar mutane 34 din Najeriya tare da bayyana cewar an dawo da mutum 25 daga cikin mutanen saboda aikata laifuka da suka hada da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma shiga kasar ta Amurka ba bisa ka’ida ba.

DUBA WANNAN: An fara: Atiku ya fara rangadin neman goyon baya don tsayawa takara, ya nada sarkin yakin neman zaben sa

Alabi ya bayyana cewar, jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da na hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP) ne suka karbi mutanen bayan saukar su.

Kazalika akwa jami’an hukumar hana shad a safarar miyagun kwayoyi a filin saukar jirgin na Legas domin karbar mutanen.

An sallami dukkan mutanen ya zuwa garuruwan su bayan hukumomin dake da ruwa da tsaki sun dauki bayanan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel