Hankula sun tashi yayin da jama’a suka ci karo da Bom a sakatariyar jam’iyyar PDP

Hankula sun tashi yayin da jama’a suka ci karo da Bom a sakatariyar jam’iyyar PDP

Rundunar Yansandan jihar Ebonyi sun bankado wani Bom da aka dasa shi a cikin sakatariyar jam’iyyar PDP na jihar, dake garin Abakili akan babban hanyar zuwa jihar Enugu inji rahoton jaridar Vanguard.

A sakamakon wannan masifa da Allah ya kawar da ita, gwamnan jihar, David Umahi ya tattaro kwamishinoninsa tare da shuwagabannin hukumomin tsaro dake jihar zuwa wani muhimmin taro a fadar gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Jerin sunayen mutane 28 da Buhari ya nadasu mukamai a fannin Shari’a

A jawabinsa bayan kammala taron, gwamna Umahi ya bayyana kaduwarsa matuka da ganin wannan bom, inda ya daura laifin akan masu adawa da gwamnatinsa, wadanda yace suna neman kwace mulki a hannunsa ko ta halin kaka.

Hankula sun tashi yayin da jama’a suka ci karo da Bom a sakatariyar jam’iyyar PDP

Umahi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamna Umahi yana cewa: “Yansanda sun gano wani Bom da aka binne a sakatariyar jam’yyarmu ta PDP, bayanai daga kwamishinan Yansandan jihar sun nuna cewar tsohon Bom ne, wanda hakan ke nuna an kwana biyu da binne shi, ina ganin a ranar da na je ofishin namu aka dasa shi, amma Allah ya hana shi tashi.

“Muna zargin yan adawa ne suka aikata wannan ta’asa, saboda burinsu su kwace mulki a hannunmu ko ta halin kaka, na umarci shuwagabannin hukumomin tsaro dasu gudanar da cikakken bincike akan lamarin, ni kuma zan garzaya wajen shugaban kasa na kai masa rahoto.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel