Zaben 2019: Har yanzu ba mu amince da Shugaba Buhari ko wani 'Dan Takara ba

Zaben 2019: Har yanzu ba mu amince da Shugaba Buhari ko wani 'Dan Takara ba

Shugaban kungiyar Kirista ta Najeriya, Rabaran Samson Ayokunle, ya yi watsi ta tuhuma gami zargi na rahotanni dake yaduwa a kafofin watsa labarai a yanar gizo dake bayyana cewa kungiyar ta ce ba bu wanda ya cancanci fadar Villa face Buhari da Oshiomhole.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kungiyar ya bayar da wannan sanarwa da sanadin Kakakin kungiyar, Fasto Adebayo Oladeji da ya bayyana a babban birnin Kasar nan na Abuja.

Oladeji yake cewa, kungiyar ta CAN (Christian Association of Nigeria) ba ta da hannu cikin rahoton goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari dake yaduwa a kafofin watsa labarai na yanar gizo.

Zaben 2019: Har yanzu ba mu amince da Shugaba Buhari ko wani 'Dan Takara ba

Zaben 2019: Har yanzu ba mu amince da Shugaba Buhari ko wani 'Dan Takara ba

Sai dai kakakin ya yi karin haske da cewa, wata kungiyar siyasa ce ta Change Advocates of Nigeria (CAN) take da alhakin wannan goyon baya ga shugaba Buhari da ake zargin kungiyar su ce sakamakon inkiyar "CAN" da ta kasance daya.

KARANTA KUMA: Yadda Tauraruwar Ronaldo ke ci ga da haskawa a gasar Kofin Duniya

Ya ke cewa, har yanzu kungiyar su ba ta aminta da shugaba Buhari a matsayin dan takarar ta ba ballantana wani dan takarar na daban a zaben 2019.

A sanadiyar haka ne ya nemi daukacin al'ummar kasar nan akan ta yi watsi da wannan ikirari tare duba da rashin alakar kungiyar su da goyon bayan shugaba Buhari da duk wata dangartaka ta amintuwa da takarar sa a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel