Zan mayar da Najeriya kasa mafi kyau a nahiyar Afrika - Shugaba Buhari

Zan mayar da Najeriya kasa mafi kyau a nahiyar Afrika - Shugaba Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tabbatarwa yan Najeriya kan burin gwamnatinsa na kawo cigaba a Najeriya

- Shugaban kasan ya ce yana son ya mayar da Najeriya kasa mafi kyawu a nahiyar Africa

- Ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take tayi aiki da duk 'yan Najeriya ba tare da la'akari da addini ko kabilanci

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa bata la'akari da addini ko kabilanci ko yanki wajen gudanar da ayyukan more rayuwar al'umma, ya kuma sake tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta dukkufa wajen kawo cigaba a Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi wannan maganen ne a ranar 20 ga watan Yuni lokacin da ya ke karaban bakuncin Khalifan Tijjaniya, Sheikh Ahmed Ibrahim Inyass a fadar Aso Rock Villa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Zan mayar da Najeriya kasa mafi kyau a nahiyar Afrika - Shugaba Buhari

Zan mayar da Najeriya kasa mafi kyau a nahiyar Afrika - Shugaba Buhari

KU KARANTA: An fara sauraran shari'ar wani Sanatan Najeriya

Legit.ng ta gano cewa shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa cigaba da aiki don cigaban kasa kuma ya yi alkawarin mayar da Najeriya kasa mafi kyawu a nahiyar Afirka da mutane za su rika ziyara.

A wata sanarwa da ya fitar, hadimin shugaban kasa a fanin kafafen yadda labarai, Garba Shehu ya ya ce shugaba Buhari ya ce: "Muna godiya da irin addu'oi da goyon baya da 'yan darikar Tijjaniya ke bawa Najeriya kuma ina son in tabbatar muku cewa gwamnatina bata nuna banbanci tsakanin yan Najeriya.

"Na san kuna yiwa Najeriya addu'an samun zaman lafiya da cigaba."

A lokacin da ya ke mika godiyarsa ga babban malamin addinin islama na kasar Senegal, shugaba Buhari ya ce kungiyoyin addini suna da matukar amfani wajen kawo cigaba a kasa.

Ya kuma ce: "Nayi matukar murna ganin yadda babban Shaihi ya yi takakiya zuwa Najeriya don ya yi ta'aziya ga iyalan marigayi Isiyaka Rabiu.

"Marigayin yana da dimbin mabiya kuma wasu daga cikinsu na zuwa Senagal kowane shekara kamar adadin mutanen da ke ziyartar Saudiyya don zuwa kabarin kakanka."

Ya kara da cewa: "Sama da 'yan Tijjaniya 40 miliyan ke yi maka addu'a kuma munyi imanin cewa Allah ne ya zabe ka don ka jagoranci Najeriya a wannan lokacin don ta kasance mai kima a idanun duniya."

Ya kuma yi addu'a samun lafiya da sa'a ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma cigaban Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel