Zaben 2019: Atiku shine zabin da zai sanya Najeriya ta fuskanci Alƙiblar ta - Ben Bruce

Zaben 2019: Atiku shine zabin da zai sanya Najeriya ta fuskanci Alƙiblar ta - Ben Bruce

Ben Murray-Bruce, Sanata Mai wakilcin mazabar Gabashin Jihar Bayelsa ya bayyana tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takara mafi cancantar zabi da zai fuskantar da Najeriya Alƙibla ta daidai.

Dan Majalisar ya bayar da wannan tabbatar wa ga tsohon mataimakin shugaban kasar ta goyon bayan inda yake cewa, al'ummar Jihar Bayelsa sun gamsu da cewar shine zabin da zai karkatar da Najeriya zuwa ga Alƙibla da za ya kai su ga gaci.

Ben Murray-Bruce

Ben Murray-Bruce

Kamar yadda shafin Jaridar Daily Trust ya bayyana, Dan Majalisar ya bayyana hakan ne yayin da Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci jihar Bayelsa domin ganawa da magoya bayan sa.

KARANTA KUMA: An tursasa ni sanya Hannu kan Kasafin Kudin 2018 - Buhari

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci fadar gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, inda ya yi wata ganawar sirrance.

Bugu da kari dan majalisar ya bayyana goyan bayan sa ga Mataimakin shugaban kasar a shafin sa dandalin sada zumunta na twitter.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel