Watakil a koma yajin aikin jami'o'i, bayan kasawar gwamnati na cimma sulhu

Watakil a koma yajin aikin jami'o'i, bayan kasawar gwamnati na cimma sulhu

- Ana barazanar koma wa yajin aiki a jami'o'i

- ASUU tace har yanzu gwamnati bata cika mata alkawarin da tayi ba

- A bara ma sunyi yajin aikin na tsawon makonni

Watakil a koma yajin aikin jami'o'i, bayan kasawar gwamnati na cimma sulhu

Watakil a koma yajin aikin jami'o'i, bayan kasawar gwamnati na cimma sulhu

Hadaddiyar kungiyar malaman jami'a ta kasa, ASUU, tace akwai yiwuwar komawa sabon yajin aiki, muddin gwamnatin tarayya bata yi gaggawar cika mata burinta ba a alkawurran da suka yi yarjejeniya a kansu a bara.

ASUU din dai ta sha shafe makonni tana yajin aiki inda komai na karatu kan tsaya cik, har sai baba-ta-gani.

Shugaban ma'aikatan jami'a marasa koyarwa zasuyi taro a ranar 4 ga watan yuli don yanke hukuncin matakin gaba da zasu dauka sakamakon rashin cika alkawari da Gwamnatin tarayya tayi musu a watanni uku da suka gabata.

Ma'aikatan sun tafi yajin aikin ne ranar 4 ga watan Disamba, 2017 akan rabon Naira biliyan 23 wanda Gwamnatin ta bawa jami'o'i a matsayin alawus.

DUBA WANNAN: An gano bayahude mai taimakon Iran da bayanan sirri

Ma'aikatan sun dakatar da yajin aikin ne a 15 ga watan Maris bayan yarjejeniya da Gwamnatin tarayya.

Duk da ma'aikatan sun bada sati 5 ne kacal don Gwamnatin ta tabbatar da yarjejeniyar, amma sunyi sati 13 shiru ba labari.

Majiyar mu ta sanar damu yanda Gwamnatin tace zata nemi biliyan 8 ta biya ma'aikatan a cikin sati 5.Matakan da gwamnatin APC ta dauka bayan karbe mulki daga hannun PDP a 2015 sun nuna za'a iya shawo kan matsalolin, sai dai ga alama, abin ya faara shan kan gwamnatin kamar dai yadda aka yi a mulkin Obasanjo a baya

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel