Kuma dai, Yan sanda sun kara da yan shi’a a Kaduna kan tsare El-Zakzaky

Kuma dai, Yan sanda sun kara da yan shi’a a Kaduna kan tsare El-Zakzaky

Wani rahoto daga jaridar Daily Sun ya nuna cewa jami’an yan sandan Kaduna sun kara da yan Shi’a a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni kan cigaba da tsare Zakzaky.

A cewar rahoton, yan shi’an dake zanga-zanga sun mamaye hanyar Ahmadu Bello, cibiyar ciniki na jihar Kaduna, dauke da kwalaye inda suka rubuta a saki shugaban su.

A hakan ne kngiyar suka gurgunta ayyuka a cibiyar birnin na tsawon wasu sa’o’i.

An tattaro cewayan sanda biyu sun ji rauni a yayin zanga-zangan wanda daga baya ya zamo rikici a cewar kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Aliyu Mukhtar.

Kuma dai, Yan sanda sun kara da yan shi’a a Kaduna kan tsare El-Zakzaky

Kuma dai, Yan sanda sun kara da yan shi’a a Kaduna kan tsare El-Zakzaky

An rahoto cewa yan shi’a da dama sun ji rauni daban-daban a yayin karon.

KU KARANTA KUMA: Tsohon IGP Gambo Jimeta bai rasu ba – Iyalansa sun tabbatar

Idan bazaku manta ba hakan ce ta kasance watanni biyu da suka shige lokacin da yan shi’a suka tada rikici bayan yan sanda sunyi kokarin hana su yin zanga-zanga a Unity Fountain Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel