Sai an sake shiri: Tosohon shugaban sojin ruwa Usman Jubrin ya kayar da EFCC a kotu

Sai an sake shiri: Tosohon shugaban sojin ruwa Usman Jubrin ya kayar da EFCC a kotu

A yau, Laraba, ne alkalin wata kotun tarayya dake Maitama, Abuja, mai shari’a Sadiq Umar, ya ki amincewa da shaidar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gabatar gaban sa a shari’ar da take yi da tsohon shugaban sojin ruwa, Usman Jubrin.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Usman tare da wasu mutane biyu; Bala Msheila, Shehu Ahmadu da kuma wani kamfani Harbour Bay International Limited bisa zargin almundahana da kuma karkatar da kudin hukumar sojin da ruwa da yawan su ya kai miliyan N600m.

Tun a ranar 22 ga watan Janairu ne kotun ta amince da bukatar lauyan Mista Umar na gudanar da shari’a cikin shari’a domin tabbatar da inganci da kuma sahihancin shaidun da hukumar EFCC ta gabatar gaban ta.

Sai an sake shiri: Tosohon shugaban sojin ruwa Usman Jubrin ya kayar da EFCC a kotu

Tsohon shugaban sojin ruwa, Usman Jubrin

Saidai bayan kamala shari’a a kan shaidun EFCC a yau, Laraba, mai shari’a Umar y ace bai gamsu cewar mutanen da suka bayar da shiada a shari’ar sun yi hakan ne bisa radin kansu ba, tare da bayyana cewar kotu ba zata karbi shaidar duk wani mutum da aka tursasa bayar da shaida ba tare da son ran sa ba.

Alkali Umar ya bayyana cewar, “bisa dogaro da abinda shaidu suka fada, a bayyane yake cewar hukumar EFCC bata gayyaci tsohon shugaban sojin rowan ba kafin gurfanar da shi.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP

Kazalika, alkali Umar, y ace hukumar EFCC ta gaza gamsar da kotun cewar mutanen da suka bayar da shaida sun yi hakan ne bisa son ran su tare da bayyana cewar, hakan ya kawo karshen shari’a cikin shari’ar da ake yi.

Mai shari’a Umar ya tsayar da ranar 27 ga wata domin cigaba da sauraron ainihin tuhumar da EFCC ke yiwa Mista Usman tare umartar hukumar ta saki dukkan takardun Mista Usman da suka hada da fasfo din shi domin samun dammar ziyartar kasar Amurka da Ingila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel