Tun a duniya: Jami'ar OAU ta kori Farfesan da ya nemi kwanciya da ɗaliba don ya bata maki

Tun a duniya: Jami'ar OAU ta kori Farfesan da ya nemi kwanciya da ɗaliba don ya bata maki

- Farfesan nan da ya nemi kwanciya da dalibarsa kafin ya kara mata kai ya fara girbar abin da ya shuku

- Yanzu haka jami'ar Obafemi Awolowo University inda anan yake koyarwa ta koresa daga aiki

Hukumar gudanarwa ta jami'ar Obafemi Awolowo University (OAU) ya sallami Farsesa Richard Akindele daga aiki sakamakon kama shi da laifin tozarta aikinsa.

Idan za'a iya tunawa Farfesan ya nemi tarawa da wata ɗalibar jami'ar ne a watannin baya kafin ya amince ya bata maki.

Tun a duniya: Jami'ar AOU ta kori Farfesan da ya nemi kwanciya da ɗaliba don ya bata maki

Tun a duniya: Jami'ar AOU ta kori Farfesan da ya nemi kwanciya da ɗaliba don ya bata maki

Shugaban jami'ar Farfesa Eyitope Ogunbodede ne ye bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taronsu a yau Laraba.

KU KARANTA: EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

Ya shaida cewa bayan kammala bincikensu, wanda shi kansa Farfesa Akindelen ya amince ya nemi ɗalibar tasa da ta ba shi haɗin kai domin ya kara mata maki don kar ta faɗi kwas ɗin da yake koyarwa, hukumar gudanarwar jami'ar yanke hukuncin korarsa.

A wata Afrilu ne dai sautin muryar Farfesan ya shahara a kafar sadarwa ta zamani inda yayi ta zagawa tsakanin mutane kuma shi ma Farfesa Akindelen tuni ya amince da cewa shi ne.

Karin wasu bayanan na nan tafe...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel