Hawaye sun kwaranya yayinda aka sada Hajiya Zainab Murtala Nyako da gidanta na gaskiya (hotuna)
Anyi jana'izar uwargidan tsohon gwamnan jihar Adamawa Hajiya Zainab Murtala Nyako a yau Laraba, 20 ga watan Yuni.
An sada marigayiyar da gidanta na gaskiya inda akayi jana'izar a garin Yola. Ta samu jama'a masu yawa da suka sallaci gawar ta.
Hajiya Zainab ta rasu ne safiyar yau Laraba bayan tayi yar gajeruwar jinya a babban asibitin FMC na garin Yola.
Ga hotunan jana'izarta a kasa:
KU KARANTA KUMA: Tsohon IGP Gambo Jimeta bai rasu ba – Iyalansa sun tabbatar
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide a shafukanmu na zumunta domin samun ingantattun labarai
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng