EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

- Dubu wani mamallakin wata kwalejin karya ya cika

- Bayan shafe sama da shekara yana yaudarar dalibai, karshe ya shiga hannun EFCC

- Har ma yanzu haka ana shirin gurfanar da shi gaban kotu

Jami'an hukumar hana cin-hanci-da rashawa ta kasa (EFCC) reshen Fatakwal dake jihar Rivers, sun cafke wani shugaban wata kwalejin share fagen shiga jami'a wanda ake zargin tana bada takardar shaidar kammala karatun ilimin horas da malamai ta NCE da kuma shaidar kammala digiri ba tare da sanin izinin hukuma ba.

EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

Wanda ake zargin mai suna John Ogbonnaya tare da wasu wanda suke tare mai suna Monday Nwapi da Miss Justina Okafor an kama su ne a garin Fatakwal inda ake zargin cewa John ya fara gudanar da kwalejin ne tun a shekara ta 2017 ba bisa ka'ida ba.

Kwalejin wadda ake zarginta da aikata laifuka daban-daban tana ba wa daliban ta karatu ne a wasu kwalejin na daban da suka hada da Brilliant international school, sai kuma kwalejin Paragon city Light.

Wannan kwaleji ta yi kaurin-suna wajen sayarwa da dalibai takardar neman cancantar shiga kwalejin (application form), sai kuma biyan kudin takardar karatu (handout) da sauran biya kudade wanda hakan ya sabawa dokar koyarwa a sauran kwalejin dake fadin tarayyar kasar nan.

KU KARANTA: Gwamanatin tarayya zata gina wuraren kiwo 94 a jahohi 10

An dai rawaito cewa Kwalejin ta fadawa daliban da suke karatu a kwalejin bayanai mabambamta game da kwalejin. Idan bayanan da suka gabata ke nuna cewa kwalejin na karkashin jagorancin wadannan makarantu ne; Kwalejin Jihar Abia, Kwalejin share fagen shiga jami'a ta Ebenezer dake garin Edda, kwalejin Jihar Ebonyi, kwalejin Enugu da kuma jami'ar garin Calabar dake jihari Rivers.

EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

EFCC ta gano wata kwalejin Bogi a garin Fatakwal

Binciken da hukumar EFCC ta gudanar ya tabbatar da cewa kwalejin ta Havana international school ba data cikakkiyar shaidar mallaka ta zama kwalejin share fagen shiga jami'a. Kuma ba tada wata alaka da sauran kwalejin da suke iƙirarin cewa tana ƙarƙashinsu.

Yanzu haka dai hukumar zata gurfanar da shugaban kwalejin a gaban kotu domin yi masa hukunci game da abinda ya aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel