Kasafin kudin 2018: Yan majalisa sun karawa kansu kudi 14.5 billion ba tare da tattaunawa da mu ba, zan aika sabon kasafin kudi - Buhari

Kasafin kudin 2018: Yan majalisa sun karawa kansu kudi 14.5 billion ba tare da tattaunawa da mu ba, zan aika sabon kasafin kudi - Buhari

Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa kan canja-canjen da majalisar dokokin tarayya tayi ckin kasafin kudin na rage-rage da kare-kare.

Buhari yace majalisar dokokin tarayya ta zabge kudi 347 billion Naira cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan kansu guda 6,403 na kimann kudi 578 billion Naira.

Kana ya tuhumci yan majalisar da karawa kansu kudi 14.5 billion ba tare da tuntubar bangaren zantarwa ba a kan hakan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018, kalli bidiyon

Shugaba Buhari yace: "Wan misali shine kasafin kudin majalisar 14.5 billion. Daga 125 billion zuwa 139.5 billion Naira ba tare wani tattauwa da fadar shugaban kasa ba.

Wani abin takaici shine wani karin da majalisar tayi na taransfa na kimanin kudi 73.96 billion Naira. Yawancin kudaden nan na albashi ne a irin wannan lokaci da gwamnati ke kokarin rage kudin albashin yan siyasa.

Duk da haka, zan sanya hannu kan kasafin kudn 2018 saboda kada a kara samun matsala cikin farfadowar tattalin arzikinmu wanda jinkirin rashin tabbatar da kasafin kudin ya janyo.

Bayan haka, ina da niyyar gyara wannan katobara da sukayi ta hanyar sake aika wani sabon kasafin kudi kuma ina kayutata zaton majalisa za tayi gaggawar tabbatarwa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel