Kasafin kudin 2018: Yan majalisa sun zabge kudi daga ayyuka da na gabatar guda 4,700 domin sanya ayyukan kansu guda 6,403 – Shugaba Buhari

Kasafin kudin 2018: Yan majalisa sun zabge kudi daga ayyuka da na gabatar guda 4,700 domin sanya ayyukan kansu guda 6,403 – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a yau Laraba, 20 ga watan Yuni 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Buhari ya nuna bacin ransa da canja-canjan da majalisar dokokin tarayya tayi ckin kasafin kudin na rage-rage da kare-kare.

Yace: “Abin takaici, babu mutunci cikin abinda suka dawo min da shi. Majalisar dokokin tarayya ta zabge kudi 347 billion Naira cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan kansu guda 6,403 na kimann kudi 578 billion Naira."

"Da yawa daga cikin ayyukan na da muhimmanci kuma zasu yi wuyan zantarwa da irin wannan zabgewa da majalisa tayi."

Wasu daga cikin sabbin ayyukan da yan majalisa suka sanya ba’a duba su da kyau ba, ba’a tsara su da kyau ba, kuma za su yi wuyan aiwatarwa.

"Bugu da kari, da yawa daga cikin ayyukan da yan majalsan dokokin tarayya suka kara cikin kasafin kudn ma’aikatu, an kara ba tare da la’akari da karfin ma’aikatun ko zasu iya ba ko kuma za su bukaci karin ma’aikata domin aiwatar da su.”

"A yanzu haka, wasu daga cikin ayyukan da yan majalisa suka kara cikin kasafin kudin hakkin jihohi ne da kananan hukumomi wanda babu ruwa gwamnatin tarayya da su."

A karshe shugaba Buhari ya ce duk da wannan abu da yan majalisa sukayi, ya rattaba hannu kan kasafin kudin domin kawar da matsalar tattalin arzikin kasa da gwamnatin ta ke karfafawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel