Wata mata ta roƙi kotu da ta umarci mijinta ya biya ta kuɗin kula masa da cikin sa

Wata mata ta roƙi kotu da ta umarci mijinta ya biya ta kuɗin kula masa da cikin sa

- Bayan rabuwa da matarsa da yayi, yanzu haka ta maka shi a kotu

- Tana bukatar ya rika biyanta kudaden da zata rika kula da kanta

- Amma sai dai ya musanta wani ikirari na tsohuwar matar tasa a gaban alkali

Wata mata mai suna Rabi Abubakar, mai dauke da cikin wata 6 ta roki wata kotu dake zamanta a yankin kubwa dake birnin tarayya Abuja da ta umarci mijinta da ya kula da ita musamman ta bangaren da ya shafi kula da juna biyun da take dauke da shi, abincin da zata ke ci da kuma kudin hayar zata ke biya.

Wata mata ta roƙi kotu da ta umarci mijinta ya biya ta kuɗin kula masa da cikin sa

Wata mata ta roƙi kotu da ta umarci mijinta ya biya ta kuɗin kula masa da cikin sa

Rabi ta bayyanawa kotun cewa sun yi aure ne bisa turbar addinin musulunci tun 29 ga watan Afrilun 2017, kuma suna zaune ne a kubwa kafin daga bisani ya tashi ya koma jihar Nassarawa da zama.

Ta ce Saleh maigidan nata ya sake bata takardar saki a ranar 24 ga watan Mayun 2017 wanda shi ne karo na biyu da yake sakin nata, daga nan ne ya kwashe komai nasa ya yi ƙaura zuwa garin keffi daje jihar Nassarawa.

Ta cigaba da bayyanawa kotu cewa tun bayan da ya sake ta ya daina kula da ita balle abinda take dauke da shi a cikinta.

KU KARANTA: Ban ji dadin canje-canjen da majalisa ta yi cikin kasafin kudin da na gabatar ba – Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa

"Gidan da nake zaune na haya ne kuma wata mai kamawa kudina zai kare, gashi Saleh ya daina kula da yaron mu balle ya bani cikakken abincin da zai gina min jiki", ta bayyanawa kotu.

Ta roki kotu da ta umarci Saleh yake bata dubu 35,000 a matsayin kudin abinci duk wata, sai kuma dubu 250,000 a matsayin kudin hayar gida da zata biya sai kuma naira dubu 11,000 a matsayin kudin da zata ke kula da juna biyun da take dauke da shi.

Sai dai ya musanta wannan tuhuma da tsohuwar matar tasa take masa, idan yace bashi da karfin da zai iya bata 35,000 duk wata saboda shi karamin ma'aikaci ne. Har wa yau yace in har da gaske ne ta kashe kudaden da take muradin a bata ya kamata ta kawo shaidar takardar da ta kashe wannan kudaden da ta ambata.

Saleh Sannan ya ce ba zai iya cigaba da biyawa Rabi kudin hayar gidanta ba sai dai ta dawo gidansa da zama.

Daga karshe alkalin kotun ya dage zaman har sai nan da 28 ga watan da muke ciki domin cigaba da sauraren shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel