Ban ji dadin canje-canjen da majalisa ta yi cikin kasafin kudin da na gabatar ba – Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa

Ban ji dadin canje-canjen da majalisa ta yi cikin kasafin kudin da na gabatar ba – Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa

-Shugaba Buhari ya nuna rashin dadinsa kan canje-canjen da majalisa tayi cikin kasafin kudin 2018

-Shugaban kasan ya rattaba hannunsa kan kasafin kudin a yau

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a yau Laraba, 20 ga watan Yuni 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Bayan rattaba hannu, Buhari ya nuna bacin ransa da canja-canjan da majalisar dokokin tarayya tayi ckin kasafin kudin na rage-rage da kare-kare.

A jawabinsa yace: "Ban ji dadin wasu canje-canje da majalisar dokokin tarayya ta yi cikin kasafn kudin da na gabatar mata ba. Hikimar kundin tsarin mulkin Najeriya na umurtan bangaren zantarwa ta gabatar da kasafin kud ga majalisa shine domin bangaren zantarwan ta ayyana muradunta."

Abin takaici, babu mutunci cikin abinda suka dawo min da shi. Majalisar dokokin tarayya ta zabge kudi 347 billion Naira cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan kansu guda 6,403 na kimann kudi 578 billion Naira."

Ban ji dadin canje-canjen da majalisa ta yi cikin kasafin kudin da na gabatar ba – Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa

Ban ji dadin canje-canjen da majalisa ta yi cikin kasafin kudin da na gabatar ba – Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa

Masu sharhi suna ganin cewa wannan dalili ne ya sanya shugaba Buhari ya jinkirta rattaba hannunsa kan kasafin kudin tun lokacin da majalisar dokokn ta mayar masa da shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel