Da yiwuwar shugaba Buhari zai gana da ‘yan sabuwar PDP - Fadar shugaban kasa

Da yiwuwar shugaba Buhari zai gana da ‘yan sabuwar PDP - Fadar shugaban kasa

- Duk da samun karuwar 'yan PDP dake dawo APC, ita ma APC na cigaba da fuskantar rikicin cikin gida

- 'Yan sabuwar PDP har yanzu ana jika wajen korafin da suke na ana yi musu wariya

- Duk da cewa shugaba Buhari ya ce ba zai zauna da su ba amma wasu bayanai na nuna akasin hakan

Duk da cewa shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya bayyana cewa ba zai gana da tsoffin ‘yan sabuwar PDP (nPDP) ba, amma kuma fadar shugaban kasar ta sake sakin wani jawabi dake bayyana cewa akwai yiwuwar zama a tattauna da su domin kawo karshen matsalar da tsagin APC dake barazanar ballewa.

Kwan gaba kwan baya: Da yiwuwar shugaba Buhari zai gana da ‘yan sabuwar PDP

Kwan gaba kwan baya: Da yiwuwar shugaba Buhari zai gana da ‘yan sabuwar PDP

A ranar Lahadi ne aka rawaito cewa shugaba Buharin ya bayyana cewa babu wata alaka tsakaninsa da turka-turkar tunda dai sha’anin ya shafi jam’iyya ne.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewa tuni an shawo kan lamarin daga can sama bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo.

Majiyar ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasar ya gana da ‘yan sabuwar PDP ne bisa umarnin shugaban kasa Buhari wanda daga baya shi kuma zai shaida masa duk yadda su kayi da su.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma

“Tuni dai har an fara tattaunawa da jam’iyyar kan wadanda suke ganin ana yi musu wariyar launin fata, har ma ana takaiga mataimakin shugaban kasa ya shiga ciki tattaunawar”. Majiyar ta bayyana.

Su dai ‘yan sabuwar PDP wasu gungun jigogin ‘yan jam’iyyar PDP ne a da da suka narke zuwa jam’iyyar APC domin cin zaben 2015. Sai dai bayan korafin sun bayar da wa’adin lallai-lallai suna son ganawa da shugaban kasa.

Daga cikinsu sun hada da; shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel