Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 73 bisa zargin yin fyade ga yarinya yar shekara 13

Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 73 bisa zargin yin fyade ga yarinya yar shekara 13

Wani tsoho mai shekaru 73, Joseph Umuluku na a hannun yan sandan Najeriya dake Warri a yanzu haka bisa zargin aikata fyade ga wata yarinya.

Wani babban jami’in dan sanda daga ofishin yansanda wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata a Warri.

Majiyar tace Umuluku, malamin tsubbu, ya kai yarinya mai shekaru 13 da haihuwa bandakin sa inda anan ne yayi lalata da ita.

Yace mai laifin da iyayen yarinyar na zama ne a gida daya a unguwar Giwa-Amu, Okumagba Layout, Warri.

Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 73 bisa zargin yin fyade ga yarinya yar shekara 13

Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 73 bisa zargin yin fyade ga yarinya yar shekara 13

A cewarsa, mai laifin ya rigada yayi Magana, inda ya kara da cewa za’a shigar da kara kotu da zaran an kammala bincike.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma

“A halin yanzu hukumar yan sanda na kokarin nemawa yarinyar magani, mai laifin yayi wasu bayanai sannan za’a tura su kotu da zaran an kammala binciken.” Cewar majiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel