Garkame tsaffin gwamnoni 2: Alkalin alkalai ya karawa alkalai karfin gwiwa

Garkame tsaffin gwamnoni 2: Alkalin alkalai ya karawa alkalai karfin gwiwa

Alkalin alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen, a jiya Talata ya yi kira ga dukkan alkalan Najeriya da su yi abinda suka ga dama kuma babu abinda zai faru.

Ya yi wannan jawabi ne yayin rantsar da sabon shugaban alkalan babban kotun tarayya, Justice Abdul Kafarati. Alkalin yace bangaren shari’a za ta tsayawa dukkan alkalin da ya nuna karfin hali wajen yanke hukunci ba tare da tsoro ba.

Game da cewarsa, bangaren shari’a zata cigaba da kasancewa yar tsakiya tsakanin bangaren zantarwa da kuma bangaren majalisa.

Yace: “Kada ku tserewa aikinki, ku kasance masu karfin hali kuma kan bakanku. Tunda ubangiji ya baka wannan matsayi, ka yi abinda ka ga yayi daidai a yanzu.”

“Ka kasance jarumi kuma mara tsoro. Babu abinda ya faru a da kuma babu abinda zai faru yanzu.”

“Saboda haka ina kira ga kai a matsayin babban alkali da kuma sauran alkalai da su dau tsatsauran matakai kuma babu abinda zai faru.”

Wannan abu na faruwa ne bayan wata alkalin babban kotun tarayya ta yankewa tsaffin gwamnonin jihar Taraba da Plateau hukuncin shekaru a kurkuku kuma a yanzu haka suna ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel