Shugaban NHIS ya shiga cikin sabon rikici na Zambar N25bn da Ma'aikatar sa

Shugaban NHIS ya shiga cikin sabon rikici na Zambar N25bn da Ma'aikatar sa

Bayan kimanin tsawon lokuta da bai wuci watanni hudu ba na rudanin mayar da Usman Yusuf bisa mukamin sa, babban sakataren ma'aikatar inshorar lafiya ta Najeriya watau NHIS (National Health Insurance Scheme) ya sake shiga cikin tsaka mai wuya dangane da zambar Naira Biliyan 25 a ma'aikatar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, sabon kwamitin kula da wanna ma'aikata, ya zargi Mista Yusuf da jagorantar ma'aikatar ta hanyar da ta sabawa doka ta gwamnatin kasar nan wajen samun yarjewar ta ta hanyar yaudara da zamba domin malalo kudi ga ma'aikatar.

Kwamitin ya kuma zargi babban Sakataren ta sabawa dokoki da shinfidar sharuddan ma'aikatar sa a yayin neman yardar gwamnatin wajen turo da kudade domin wasu aikace-aikacen tsaro na hukumar.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole, ya dakatar da Mista Yusuf daga mukamin sa a watan Yulin shekarar 2017 da ta gabata sakamakon tuhumar ma'aikatar sa na sabawa ka'aidojin ta.

Shugaban NHIS ya shiga cikin sabon rikici na Zambar N25bn da Ma'aikatar sa

Shugaban NHIS ya shiga cikin sabon rikici na Zambar N25bn da Ma'aikatar sa

Bugu da kari Ministan ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike akan Mista Yusuf dangane da wannan zargi da tuhumce-tuhumce na ma'aikatar sa kuma ta tabbata ya tafka kura-kurai da suka sabawa ka'ida kuma ya mika sakamakon zuwa ga fadar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya nemi goyon bayan Gwamna Dickson, ya yi alkawarin sauya fasalin Najeriya

Sai dai a yayin haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mai she da Mista Yusuf bisa kujerar sa ba tare da tuntubar Ministan Lafiya ba wanda hakan ya janyo cecekuce gami da zanga-zanga a ma'aikatar na nuna rashin goyon baya sakamakon dawowar sa.

Daga bisani kuma shugaba Buhari ya kirayi Ministan da Yusuf domin wata ganawa inda ya umarce su a kan abinda ya riga da faruwa ya faru saboda haka su sabunta dangartakar su domin ci gaban ma'aikatar ta lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel