Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kotu ta garkame shi

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kotu ta garkame shi

Wata kotun majistare da ke zaune a Ile-ife jihar Osun ta garkame wani tsoho dan shekaru 72 a kurkuku a ranan Talata, 19 ga watan Yuni kan laifin yi wa wata wanka da ruwan Acid.

Tsohon mai suna, Adegboye Emmanuel, wanda aka gurfanar kan laifin niyyar kisan kai da keta akan matan zai ci gidan kurkuku duk da cewan ya musanta wannan zargi da ake masa.

Alkalin majistaren, Ishola Omisade, ya yi watsi da belin da lauyan Emmanuel, Mr Bolaji Adewale, ya nema. Ya ce wajibi ne a garkame mai laifin a kurkukun Ile-ife.

KU KARANTA: Tirela dauke da Katako ta kashe jama’a a Legas bayan ta fado daga saman gada

Lauyan gwamnati, Insp Emmanuel Abdullahi, ya bayyanawa kotu cewa an aikata wannan laifi ne ranan 6 ga watan Yuni misalin karfe 9 na safe a Oluorogbo phase III on Ondo road, Ile-Ife.

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kotu ta garkame shi

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kotu ta garkame shi

Lauyan yace Emmanuel ya yi kokarin kashe matar mai suna Abayomi Veronica ta hanyar watsa mata wani ruwa da ake kyautata zaton ruwan acid ne wanda ya ji mata mumunan rauni a jiki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel