Yaki da rashawa: Ka binciki kudin kamfen dinka na 2015 – PDP ga Buhari

Yaki da rashawa: Ka binciki kudin kamfen dinka na 2015 – PDP ga Buhari

Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna adalcinsa wajen yaki da rashawa ta hanyar bincikar tushen kudin kamfen dinsa na zaben 2015.

Babban sakataren PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan wanda ya bayyana hakan a bikin ranar Ogidi 2018, a karamar hukumar Ogidi, Ijumu dake jihar Kogi yayi ikirarin cewa abun mamaki ne yadda shugaban kasa k eta Magana kan batun yaki da rashawa da gefen bakinsa guda biyu.

Ologbondiyan yace: “Yadda shugaban kasar ke Magana yana ba mu yan PDP mamaki saboda mun yarda cewa a shugaban kasar na yiwa barayin kusa das hi rufa-rufa sannan kuma mun yarda cewa idan har shugaban kasar na adalci kan yaki da rashawa toh ya bayyanawa jama’a yadda aka tattara kudaden yakin neman zabensa na 2015.

Yaki da rashawa: Ka binciki kudin kamfen dinka na 2015 – PDP ga Buhari

Yaki da rashawa: Ka binciki kudin kamfen dinka na 2015 – PDP ga Buhari

"Ya fada mana wadanda suka harhada kudi, amma idan yaki aikata hakan, toh shugaban kasar baida wata daman a tsayawa ya zargi ko wani dan Najeriya da aikata sata.

“PDP na kalubalantar shugaban kasa da ya bayyana yadda aka samu kudin kamfen dinsa a 2014 sannan ya fada mana nawa mutanen suka harhada.”

KU KARANTA KUMA: Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara

Da yake Magana kan shirin tsoffin mambobin jam’iyyar dake shirin dawowa PDP, Ologbodiyan yace kofa a bude take ga kowa day a shirya ceto kasar daga hannun APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel