Damfara: Hukumar EFCC ta fitar da sabuwar sanarwa ga 'yan Najeriya

Damfara: Hukumar EFCC ta fitar da sabuwar sanarwa ga 'yan Najeriya

Shugaban babban ofishin shiyya na hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) dake garin Fatakwal na jihar Ribas, Nnaghe Itam ya gargadi al'ummar Najeriya da su bi a hankali da 'yan damfara.

Mista Nnaghe Itam ya bayyana cewar kiran ya zama dole ne ganin yadda wasu bata gari ke zuwa suna yin badda-kama suna yaudarar mutane musamman masu hannu-da-shuni cewar wai su za su samar masu da kwangila a ma'aikatar rayawa da cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission (NDDC).

Damfara: Hukumar EFCC ta fitar da sabuwar sanarwa ga 'yan Najeriya

Damfara: Hukumar EFCC ta fitar da sabuwar sanarwa ga 'yan Najeriya

KU KARANTA: Buhari zai rabawa talakawa kudin satar Abacha

Legit.ng ta samu cewa shugaban ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Talatar da ta gabata a yayin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na hukumar a can garin na Fatakwal.

A wani labarin kuma, Haramtattun kaya na akalla sama da Naira biliyan 1.3 ne jami'an rundunar hukumar kwastam ta kasa suka kama tun daga tsakiyar watan jiya ya zuwa farkon wannan watan da muke ciki na Yuni kamar dai yadda kwanturolan shiyya ta 'A' Mohammed Uba ya shaidawa majiyar mu.

Mohammed Uba ya bayyana wadannan alkaluman ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake a garin Ikeja, jihar Legas inda ya bayyana cewa cikin haramtattun kayayyakin hadda motocin alfarma 15 da suka kai darajar Naira miliyan 383.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel