Assha: 'Yan bindiga sun sace wani babban ma'aikacin NNPC

Assha: 'Yan bindiga sun sace wani babban ma'aikacin NNPC

- An ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun sace John Ihenacho a garin Ndoki dake karamar hukumar Oyigbo a Jihar Rivers

- Sai dai an kashe Ihenacho bayan an biya 'yan bindigan kudaden fansa masu yawa

- Hukumar yan sanda ta ce an kama wasu da ke tsamanin suna da hannu cikin kisar

Wasu gungun 'yan barandan sun sace wani babban ma'aikacin ma'aikatan man fetur ta Najeriya (NNPC) mai suna John Ihenacho, sai dai bayan yan barandan sun karbi kudaden fansa daga iyalansa, sun kuma kashe shi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa 'yan barandan sun sace shi ne a unguwar Ndoki da ke karamar hukumar Oyigbo dake Jihar Rivers kafin suka kashe shi.

Assha: 'Yan bindiga sun sace wani babban ma'aikacin NNPC

Assha: 'Yan bindiga sun sace wani babban ma'aikacin NNPC

KU KARANTA: 'Yan sandan Legas sun bankado wata makarkashiyar sace ma'aikaciyar kwastam

Kamar yadda rahoton ya bayyana, sun haka kabari sun birne marigayin.

Kakakin hukumar Yan sanda na Jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutane.

Omoni ya ce a yayin da ake musu tambayoyi ne suka amsa aikata laifin kana suka kai yan sanda kabarin da suka birne mamacin.

"Ina mai tabbatar muku da cewa an kama wasu daga cikin wanda suka aikata laifin kuma ana cigaba da bincike.

"Hukumar yan sandan jihar Rivers tana cigaba da neman sauran wadanda ke da hannu cikin kissan jami'in NNPC din," inji shi.

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda babban hafsin sojin kasa, Laftanat Janar Tukur Buratai ya umurci sojoji su kara zage damtse wajen ganin sun magance matsalar garkuwa da mutane da satar shanu.

Buratai ya yi wannan kira ne lokacin da ya ke mika sakon murnar sallah karama na shekarar 2018 ga sojojin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel