Jami'an kwastam sun kama haramtattun kaya na sama da Naira biliyan 1.3

Jami'an kwastam sun kama haramtattun kaya na sama da Naira biliyan 1.3

Haramtattun kaya na akalla sama da Naira biliyan 1.3 ne jami'an rundunar hukumar kwastam ta kasa suka kama tun daga tsakiyar watan jiya ya zuwa farkon wannan watan da muke ciki na Yuni kamar dai yadda kwanturolan shiyya ta 'A' Mohammed Uba ya shaidawa majiyar mu.

Mohammed Uba ya bayyana wadannan alkaluman ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake a garin Ikeja, jihar Legas inda ya bayyana cewa cikin haramtattun kayayyakin hadda motocin alfarma 15 da suka kai darajar Naira miliyan 383.

Jami'an kwastam sun kama haramtattun kaya na sama da Naira biliyan 1.3

Jami'an kwastam sun kama haramtattun kaya na sama da Naira biliyan 1.3

KU KARANTA: Buhari ya samu kishiya a zaben 2019

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa yanzu dai kama ta kammala shirye-shiryen duk da suka wajaba domin fara anfani da fasahar makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki ga 'yan kasar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Mista Dmitry Shornikov da ke zaman babban masani kuma jami'an dake da kula da harkokin fasahar nukiya na kasar Rasha ya fitar ya turawa majiyar mu a ranar Talatar da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel