Buhari zai rabawa 'yan Najeriya Dala miliyan 322 da Abacha ya sata

Buhari zai rabawa 'yan Najeriya Dala miliyan 322 da Abacha ya sata

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sun ce yanzu haka dai suna kan matakin karshe ne domin rabawa 'yan Najeriya kudaden su da tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Abacha ya sata ya kai kasar waje.

Wani dai na hannun damar shugaban kasar ne Mai shari'a Ibekaku Nwagwu ya bayyana wa manema labarai hakan a garin Abuja, babban birnin tarayya.

Buhari zai rabawa 'yan Najeriya Dala miliyan 322 da Abacha ya sata

Buhari zai rabawa 'yan Najeriya Dala miliyan 322 da Abacha ya sata

KU KARANTA: Moghalu ya cancanci ya shugabanci Najeriya - Sarki Sanusi

Legit.ng ta samu cewa Mista Ibekaku ya ce da zarar sun kammala shirin su, za su rabawa 'yan Najeriya da suka fi talauci kudaden ne ta hanyar sabbin tsare-tsaren da suke kan shiryawa.

A wani labarin kuma, Haramtattun kaya na akalla sama da Naira biliyan 1.3 ne jami'an rundunar hukumar kwastam ta kasa suka kama tun daga tsakiyar watan jiya ya zuwa farkon wannan watan da muke ciki na Yuni kamar dai yadda kwanturolan shiyya ta 'A' Mohammed Uba ya shaidawa majiyar mu.

Mohammed Uba ya bayyana wadannan alkaluman ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake a garin Ikeja, jihar Legas inda ya bayyana cewa cikin haramtattun kayayyakin hadda motocin alfarma 15 da suka kai darajar Naira miliyan 383.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel