Bashi da wani tasiri a siyasar Kano – Ganduje ya yi tone-tone a kan rikicin sa da Kwankwaso

Bashi da wani tasiri a siyasar Kano – Ganduje ya yi tone-tone a kan rikicin sa da Kwankwaso

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da maganar cewar tsohon gwamna Kwankwaso yana da tasiri har yanzu a siyasar jihar.

Ganduje ya furta hakan ne a gidan jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon dan siyasa, Malam Musa Gwadabe, a jiya, Laraba.

Allah ke bayar da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, kamar yadda shine kadai keda ikon karbar mulki a hannun duk wanda ya so. Mu mun mika al’amuran mu ga Allah, a saboda haka babu wani mutum, komai mukamin sa kuma ko a ina yake, da zai hana mu yin nasara a zabukan mu. Nasara daga Allah take,” a kalaman Ganduje.

Bashi da wani tasiri a siyasar Kano – Ganduje ya yi tone-tone a kan rikicin sa da Kwankwaso

Ganduje da Kwankwaso

Ganduje ya cigaba da cewa, “duk wanda yake tunanin zai yake mu, mun shirya masa. Mun yi zaben kananan hukumomi kuma mun yiu nasara ba tare da samun tashin hankali ba. Akwai lokutan da a baya aka sha samun barkewar rikici bayan kamala zabukan kananan hukumomi amma mu a lokacin mu ba a samu haka ba.”

DUBA WANNAN: Katobara: Allah-n da ya yi mana maganin mulkin Abacha, shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo

A nasa jawabin, Musa Gwadabe, y ace sun dade suna bawa gwamna Ganduje shawarar ya kasance mai hakuri da abinda zai gani tare da nuna jin dadin sa cewar har yanzu gwamnan na aiki da shawarar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel