Rai bakon Duniya: An tsinci gawar yara 5 tare da na mahaifiyarsu, Ubansu ya tsallake rijiya da baya

Rai bakon Duniya: An tsinci gawar yara 5 tare da na mahaifiyarsu, Ubansu ya tsallake rijiya da baya

Wata Mata da yayanta guda biyar sun yi mutuwar ban tausayi a gidansu dake layin Akpata cikin karamar hukumar Egor na jihar Edo, a sakamakon hayakin na’urar bada wuta, wato Janareta da suka shaka yayin da ya cika musu daki, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutum daya ne kawai ya sha, shi ne Mahaifin yaran, Tochukwu Okwueze wanda shi ma a yanzu haka yana nan kwance rai fakwai mutu fakwai a Asibiti, bayan cetoshi da aka yi yayin da aka balla kofar dakin nasu.

KU KARANTA: Tirela dauke da Katako ta kashe jama’a a Legas bayan ta fado daga saman gada

Rai bakon Duniya: An tsinci gawar yara 5 tare da na mahaifiyarsu, Ubansu ya tsallake rijiya da baya

Hayaki

Zuwa yanzu dai an garzaya da gawarwakinnasu zuwa dakin ajiyan gawa na wani babban asibiti dake garin, kamar yadda Kwamishinan Yansandan jihar, Johnson Kokumo ya bayyana.

Wani dan uwan mamatan mai suna Vincent yace shi kanin Mijin ne, kuma karamin kaninsu ne ya kira shi daga Legas, inda ya fada masa cewa ibtila’I ya fada ma yayansu, don haka ya kira ya ji abinda ke faruwa.

“Da jin haka sai na kira matar yayana, sai kawai na ji wani murya yana fada min wai mai wayar da yayanta biyar sun kwanta barci basu tashi ba. Amma Yansanda sun fada min cewa idan jikin yayana yayi kamari zasu neme ni.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel