Tirela dauke da Katako ta kashe jama’a a Legas bayan ta fado daga saman gada

Tirela dauke da Katako ta kashe jama’a a Legas bayan ta fado daga saman gada

Wata babbar Motar Tirela dauke da tarin katako ta yi sanadin mutuwar jama’a a jihar Legas yayin da ta rikito daga saman gadar Ojuelgba na jihar Legas, inji rahoton gidan Talabijin na Channels.

Wannan mummunan hadari ya faru ne a daren Talata, 19 ga watan Yuni da misalin karfe 8:30, wanda shi ne lokaci na hudu kenan da ake samun babbar mota na fadowa daga kan gadan a cikin shekaru biyu.

KU KARANTA: Wani karamin Yaro ya gamu da ajalinsa a cikin wani Kududdufi a jihar Kano

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Tirelan ya fado ne akan wasu motocin Bas guda uku dake dauke da Fasinjoji, da kuma wata karamar Mota guda daya, inda har yanzu ba’a tantance adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas. LASEMA da na hukumar kiyaye haddura ta kasa da jami’an Yansanda sun isa wajen, inda suke gudanar da aikin bada agajin gaggawa, sakamakon hanyar ta cushe, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Motar na tsananin gudu ne a lokacin da wannan mummunan hatsari ya auku, wanda hakan ke nuna ga gangancin da direban Motar ke yi a yayin tuki. Sai dai a jawabin shugaban LASEMA, yace sun gano gawawarkin mutane biyu ne kadai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel