Rundunar Sojoji ta yi ram da yan bindigan da suka kashe hadimin wani Gwamna

Rundunar Sojoji ta yi ram da yan bindigan da suka kashe hadimin wani Gwamna

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da kama gungun yan bindiga guda uku da suka hallaka hadimin gwamnan jihar Benuwe, Denen Igbana, mai bai shi shawara akan al’amuran tsaro, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamandan yaki dake jihar Benuwe, Manjo janar Adeyemi Yekinine ya sanar da haka a ranar Talata 19 ga watan Yuni a garin Makurdi, inda yace Sojoji sun kama yan bindigan ne yayin da suke tserewa daga wani ruwan wuta da sha daga hannun Sojoji.

KU KARANTA: Wani karamin Yaro ya gamu da ajalinsa a cikin wani Kududdufi a jihar Kano

Ida ba’a manta ba, a shekarar 2016 ne yan bindiga suka dirka ma Igabana bindiga a kirji yayin da yake tare da iyalinsa a gida.

Rundunar Sojoji ta yi ram da yan bindigan da suka kashe hadimin wani Gwamna

Marigayi Igbana

Sai dai Yekini bai bayyana sunayen mutanen ba, amma ya tabbatar ma yan gudun hijira na jihar cewa zasu koma gidajensu nan bada jimawa ba, sakamakon namijin kokari da Sojoji ke yin a ganin sun kakkabe duk wani sansanin yan bindiga dage jihar.

A wani labarin kuma, Sojoji sun hallaka yan bindiga guda Arba’in a wani samame na musamman da suka kai mabuyarsu dake cikin dazukan jihohin Benuwe da Nassarawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel