Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi

Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana gwamnatin tarayya ta bayar da wani gargadi da jan kunne mai ban tsaro dangane da amfani da shinkafa 'yar Thailand inda ta ce ba bu abin da ta kunsa face guba mai haifar da cutar daji.

Ministan noma da raya karkara na Najeriya, Cif Audu Ogbeh, shine ya bayar da wannan gargadin a ranar Litinin din da ta gabata yayin ganawa da wasu matasa a babban birnin kasar nan inda ya bayyana cewa, mafi akasarin mutane sun kulla soyayya da shinkafa 'yar Thailand sakamakon shaharar ta sai dai tabbas tana kunshe da sunadarin guba.

Yake cewa, akwai sunadarin Arsenic da yake yaduwa a cikin gonakin da aka shafe shekaru da shekaru a na gudanar da noman shinkafa wanda a sanadiyar hakan ne yake kara habaka kuma shi sunadarin Arsenic yana haifar da cutar Daji watau Kansa.

Legit.ng ta fahimci cewa, irin su jihar Delta da wasu kasashe dake yankin Kudu maso Gabashin nahiyyar Asia akan samu ire-iren wannan habaka ta sunadarin Arsenic a gonakin su sakamakon yawaitar noman shinkafa da ba bu kakkautawa.

Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi

Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi

Ya ci gaba da cewa, a kwana-kwanan nan za a rufe iyakokin kasar nan na dindindin domin dakile fasakaurin shinkafa daga kasashen ketare da sauran ababe masu dauke da sunadarin guba zuwa cikin Najeriya.

Ministan ya kara da cewa, daya daga cikin ababe masu rusa tattalin arzikin Najeriya shine shigo da shinkafa daga kasashen ketare wanda cikin 'yan kwanaki kadan za a dakatar da hakan domin kare lafiyar al'umma da kuma tattali arzikin kasa.

KARANTA KUMA: Ana haihuwar Yara 150, 000 da cutar Amosanin Jini a kowace shekara - Babadoko

Ogbeh ya kuma bayyana damuwar sa dangane da yadda alakar dake tsakanin Najeriya da wasu makotan kasashe na nahiyyar Afirka ke janyo nakasun tattalin arzikin kasa da ya sanya aka yanke shawarar rufe iyakokin ta.

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata gwamnatin tarayya ta sama babbar nasara wajen raguwar shigo da shinkaffa da kaso 95 cikin 100 tare da ƙara adadin manoman shinkafa.

Ya kara da cewa, akwai jihohin da suka yi hobbasa wajen noman shinkafa da suka hadar da Anambra, Ebonyi, Kebbi, Kano da kuma Jigawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel