An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

An kama gagararren dan fashi kuma mai garkuwa da mutane, Omote Eboh, a wani surkukin daji da yake buya bayan ya kasha dan majalisar jihar Delta, Honarabul Onokpama, duk day a karbi kudin fansar garkuwa da shi har N500,00.

An samu gawar Honarabul Onokpama bayan jami’an ‘yan sanda sun shafe kwanaki biyu suna neman sa a dajin Okurekpo dake karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta.

An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

Mai garkuwa da mutane, Emboh

Honarabul Cif Evance Ochuko, abokin dan majalisar da aka kashe ne ya jagorancin tawagar jami’ar tsaro da ‘yan bijilanti da mafarauta da suka samu nasarar kama dan ta’adda Eboh a maboyar sa dake jihar Edo.

DUBA WANNAN: Ka janye sojoji daga Maiduguri, ka tura ‘yan sandan SARS –An yiwa buhari zanga-zanga

Eboh da yaran sa sun sace dan majalisar, Honarabul Onose, tare da boye shi a wani surkukin daji a Okurekpo dake karamar hukumar Ethiope ta Gabas kafin daga bisani su harbe shi.

An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

Yayin neman gawar Dan majalisar da aka kashe

An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

Surkukin dajin da aka samu gawar dan majalisar

An kama mai garkuwa da mutane da ya kashe dan majalisa bayan karbar kudin fansa N500,000, hotuna

Gawar dan majalisa da ta fara zagwanyewa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel