Ekiti: Gangamin APC babu wani abun kirki sai borin kunya – PDP

Ekiti: Gangamin APC babu wani abun kirki sai borin kunya – PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana gangamin neman kujerar gwamna da jam’iyyar APC tayi a dakin taron Olufemi Kayode Stadium, Ado-Ekiti a ranar Talata a matsayin nuna gazawa a jam’iyyar.

Jam’iyyar adawan ta bayyana cewa wadanda sukayi Magana a taron basu bayyana ko wani shiri mai muhimmanci da APC tayiwa mutane jihar ba, cewa hakan ya nuna bata da wani yunkuri da zatayi sai yaudara da karya.

Ekiti: Gangamin APC babu wani abun kirki sai borin kunya – PDP

Ekiti: Gangamin APC babu wani abun kirki sai borin kunya – PDP

A sanarwar da PDP ta fitar tab akin kakkainta na kasa, Kola Ologbondiyan tace babu abunda shugabannin APC suka yi sai jifar Ayo Fayose da kalamai.

KU KARANTA KUMA: An yankewa iyaye masu shayarwa 3 da wasu mutane biyu daurin watanni shida gidan yari kan laifin satar kaji na kimanin N3.2m

“Wannan hujja ce na cewa Dr Fayemi ba zai iya bayyana nasarorinsa ba a lokacin da yake kujerar mulki, wanda akai ne zai so a sake zabarsa.” Cewar PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel