Dakarun Sojin Najeriya 9 sun gamu da ajalinsu a hannun mayakan Boko Haram

Dakarun Sojin Najeriya 9 sun gamu da ajalinsu a hannun mayakan Boko Haram

Mayakan rundunar Boko Haram sun hallaka dakarun Sojin Najeriya tara a yayin wata karanbatta da suka sha yi a garin Gajiram dake jihar Borno, kamar yadda wasu jami’an Soji suka tabbatar ma jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan hari ya faru ne a garin Gajiram dake kimanin kilomita 80 daga birnin Borno da misalin karfe 2 na ranar Litinin, 18 ga watan Yuni, inda da fari hukumar Yansandan jihar tace hadakar Yansanda da Sojoji sun yi bata kasha da yan ta’adda, amma ba’a kashe kowa ba, inji ta.

KU KARANTA: BMasha Allah: Buhari ya bullo da hanyoyi 6 na kawo karshen kashe kashe tsakanin Manoma da Makiyaya

Sai dai kamfanin dillancin labaru na AFP ta gano wani sako da rundunar Yansandan ta aike, wanda ke nuna an kashe jami’ai tara and jikkata jami’ai biyu. Haka zalika mazauna kauyukan sun tabbatar da ganin yan Boko Haram guda 12 makare a cikin wata Mota.

Garin Gajiram ya sha fuskantar hare haren ta’addanci, inda a shekarar da ta gabata wasu yan ta’adda suka kashe Sojoji bakwai, ana zargin tsagin Boko Haram na Mus’abu Albarnawi da kaiwa.

A wani labarin kuma, wasu kananan yara mata su shida sun tayar da bama bamai a harin kunar bakin wake da suka kai garin Damboa, inda suka kashe mutane arba’in da uku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel