2019: Atiku ya nemi goyon bayan Gwamna Dickson, ya yi alkawarin sauya fasalin Najeriya

2019: Atiku ya nemi goyon bayan Gwamna Dickson, ya yi alkawarin sauya fasalin Najeriya

Tsohon Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa ga gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP inda ya nemi goyon bayan su a zaben 2019.

Alhaji Atiku wanda ya isa fadar gwamnan dake Birnin Yenagoa da misalin karfe 12.00 na ranar yau ta Talata, ya kuma gabatar da wasu takardu ga gwamna Dickson dangane da tsare-tsaren sa na sauya fasalin kasar nan da ya ce shine tafarkin hadin kai da ci gaba a Najeriya.

Tawagar tsohon Mataimakin shugaban kasar ta hadar da tsohojn gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenge Daniels, tsohon Ministan harkokin Neja Delta, Elder Godspower Orubebe da sauransu.

Bayan gudanar da wata ganawar sirrance ta sa'o'i kalilan tare da gwamnan, Alhaji Atiku ya kuma dugunzuma zuwa Sakateriyar jam'iyyar PDP dake jihar inda magoyan bayan sa suka yi ma sa lale maraba.

2019: Atiku ya nemi goyon bayan Gwamna Dickson, ya yi alkawarin sauya fasalin Najeriya

2019: Atiku ya nemi goyon bayan Gwamna Dickson, ya yi alkawarin sauya fasalin Najeriya

Da yake jawabi ga magoya bayan jam'iyyar, Atiku ya yabawa gwamna Dickson dangane da ci gaba da ya kawowa jihar sa tare da godiya ga al'ummar da suka bayar da dama ta ci gaba da riko da jam'iyya daya a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya taya Mahaifin Okonja-Iweala murnar cika shekara 90 a Duniya

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da cewa, ya sake dawowa jihar ne domin sabunta mu'amala da inganta alakar dake tsakanin sa da al'ummar jihar Bayelsa tare da neman goyan bayan su dangane da zaben 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, Atiku ya kuma yabawa gwamna Dickson dangane da ya jajirce wajen fafutikar sauya fasalin kasar nan da bai gushe ba wajen kira akan hakan tun shekaru 14 da suka gabata.

A nasa jawaban, Gwamna Dickson ya bayyana cewa Atiku jigo na siyasa tare da jaddada cewar zaben shugaban kasa na 2019 zai kasance raba gardama akan sauyan fasalin kasar nan inda ya yi kira ga dukkanin mambobin jam'iyyar PDP akan tashi tsaye wajen kwatar mulki daga hannun gwamnatin APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel