Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya fadi wurare biyu da ya kamata sojojin Najeriya su kai simame domin a cewarsa wuraren na mayakan Boko Haram ke girke.

A cewarsa, wuraren da mayakan Boko Haram din ke buya sune yankunan Damboa/Gwoza/Chibok da kuma yankin tafkin Chadi.

Ndume ya yi kira da sojojin Najeriya su mayar da hankali a wuraren biyu da ya lissafa muddin idan suna son su ci galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram a jihar ta Borno.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ce ba zai gana da mambobin nPDP ba, ya bayar da dalilinsa

Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

Sanatan Najeriya ya fadi wuri biyu da ya kamata sojoji su nemi mayakan Boko Haram

A yayin da ya ke tsokaci a kan harin da Boko Haram su kai a karamar hukumar Damboa, Ndume ya jadada cewa ya samu rahoto daga amintaten majiya cewa wurare biyun da ya fadi ne inda yan kungiyar Boko Haram ke buya.

Ya kara da cewa muddin sojojin Najeriya suka kai hari a wurare biyun da ya lissafa, za'a karya lagwan kungiyar ta Boko Haram.

"An ruwaito cewa Abubakar Shekau da ke jagorantar bangare daya na kungiyar Boko Haram yana zaune ne a yankin Chibok yayin da shi kuma Mamman Nur da tawagarsa suna zaune ne a yankin tafkin Chadi," inji Ndume.

Ya ce idan sojojin su kayi amfani da makaman da suka mallaka za su iya cin galaba a kan yan ta'addan.

"Suyi kokari su kore mana yan ta'addan domin mu samu zaman lafiya. Wadannan wuraren ne aka bayar da rahoton cewa mayakan Boko Haram na zaune" inji shi.

Baya ga ta'aziyya da ya yi ga iyalan wadanda aka kashe a harin Damboa, Ndume ya kuma kara da cewa ya tura wakilai su kai ziyara ga wadanda suka sami rauni a asibitoci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel