An haramtawa jami'an tsaro amfani da shafukan sada zumunta

An haramtawa jami'an tsaro amfani da shafukan sada zumunta

Rahotanni sun kawo cewa Gwamnatin kasar Kamaru ta hanawa jami'an tsaro na Jandarma amfani da shafukan sada zumunta irin su WhatsApp, Facebook da kuma Twitter.

Karamin ministan tsaro na kasar wanda ya kafa wannan doka, ya kuma bukaci jami'an tsaro da su rufe zaurukan mahawarori da na kulla zumunta da suka bude.

Sannan kuma an haramtawa jami'an yin amfani da wayoyin hannu na Android.

Wannan hukuncin ya biyo bayan abin da mai magana da yawun Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya kira bata wa jami'an tsaro suna ba tare da dalili ba.

Hakazalika an bukaci daidaikun jami'an tsaron da suka bude shafukan karan-kansu a Facebook da Twitter da WhatsApp da hakan ke tantance su a matsayinsu na jami'an tsaro da su rufe su.

KU KARANTA KUMA: Wani babban Fasto ya bayar da N1m domin a kammala ginin Masallaci a Calabar

Karamin ministan ya dauki wannan matakin ne domin takaita bayyana wasiku, da kuma wasu tsare-tsare na sirri da Gwamnati ke yi daga fadar Shugaban kasa zuwa ma'aikatar tsaro.

A wani lamari na daban munji cewa dakarun hukumar soji, runduna ta 93 sun yi nasarar kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ta’addanci ne da suka dade suna tayar da hankula da mutane a yankin Katsina Ala da kewaye.

An kama su ne bayan samun bayanan sirri. Amakaman da aka samu a hannun ‘yan ta’addar sun hada da; karamar bindiga daya, wata bindigar gida guda daya, carbi bakwai na alburusai da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu domin samun ingantattun labarai:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel