Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP

Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rahidi Ladoja, ya bayyana cewar ba zai mayar da ko sisi aljihun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) dake binciken sa bisa aikata badakala da almundahana da kudin jama’a lokacin da yake gwamna ba.

Ya bayyana cewar bai saci ko sisi ba lokacin da yake mulki, a saboda haka ba zai mayar da abinda bai dauka ba.

A kwanan nan ne wani mai yiwa hukmar EFCC bincike, Abubakar Madaki, ya shaidawa kotu cewar, Ladoja, ya bayar da umarnin sayar da hannayen jarin jihar da darajar su ta kai biliyan N6.6bn a kan farashi mai rahusa ba tare day a tuntubi majalisar zartarwa ta jihar sa ba.

Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP

Tsohon gwamnan PDP Rashidi Ladoja

Da yake bayar da shaida a gaban kotu, Madaki, ya bayyana cewar kudin sayar da hannayen jarin ya shiga aljihun Ladoja ne da na wasu dangin sad a abokai. Zargin da Ladojan ya ki amincewa das hi tare da kafewa kan cewar bai saci kudi ba lokacin da yake gwamna.

DUBA WANNAN: An kara gano wasu makudan biliyoyi da aka boye

Da ayke ganawa da manema labarai jim kadan bayan dawowar sa daga sallar idi ranar juma’a a gidan sa dake garin Ibadan, Ladoja ya bayyana cewar, “da gaske ban mayar da ko sisi aljihun hukumar EFCC ba saboda ban saci komai ba kuma ba zaka iya mayar abun dab aka dauka ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel