Masu zanga-zanga sun zagaye Hedikwatar APC a Abuja

Masu zanga-zanga sun zagaye Hedikwatar APC a Abuja

Dubban masu zanga-zanga sun mamaye babban ofishn jam’iyyar APC na kasa dake babban birnin tarayya.

Masu zanga-zangar sun kasance dauke da kwalayen da ke kunshe da rubutun neman a dakatar da shugabannin da ke ci a yanzu, karkashin jagorancin John Odegie-Oyegun, wadanda ya kamata su sauka idan an zo gangamin jam’iyyar na kasa a ranar Asabar mai zuwa.

Hakazalika, masu zanga-zangar, su na kuma dauke da kwalayen da ke nuna jinjina ga babban dan takarar shugabancin jam’iyya daya tilo, tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshimhole.

Masu zanga-zanga sun zagaye Hedikwatar APC a Abuja

Masu zanga-zanga sun zagaye Hedikwatar APC a Abuja

Wa’adin su Oyegun dai zai kare ne a ranar Asabar mai zuwa idan an zo taron gangamin jam’iyya, domin a ranar ce za a zabi sabbi shugabannin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Sarki Sanusi ya goyi bayan wani dan takarar shugaban kasa ba Buhari ba

A halin da ake ciki Sanata Shehu Sani wanda ya kasance mai hamayya da gwamnan jiharsa, Nasir El-Rufa’I, ya yi bayani ga manema labarai a gidansa da ke Kaduna ranan Litinin.

Yace jam’iyyarsa ta APC tana yi abubuwan da take sukan PDP da yi kafin ta hau gwamnati kuma idan ba’a dau mataki ba zasu fice daga jam’iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel