PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

- Jam'iyyar PDP na cigaba da asarar mambobinta masu rike da mukamai

- A yau ma dan majalisar jihar Ekiti Adeniran Alagbadaya fice daga jam'iyyar ta PDP

- Kafin shi,wani dan majalisar jihar shi ma ya fice gabanin zaben gwamnan da za'a yi a jihar

Jirgin sauya sheka daga PDP zuwa APC ya dira a jihar Ekiti, inda yayi awon gaba da Adeniran Alagbada dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Ise/Orun.

Adeniran Alagbada dai shi ne mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin kasa da gidaje.

PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

Da yake sanar da ficewar ta shi daga PDP zuwa APC yayin wani taron manema labarai a babban birnin jihar Ado-Ekiti a yau Talata, Alagbada ya ce mutanen mazabarsa suna goyon bayan wannan mataki da ya dauka.

Ya kuma kara da cewa mutanen mazabarsa sun fusata bisa rashin cika alkawarin da gwamnan ya dauka na basu damar fitar da dan takarar gwamna daga yankin nasu a 2018. Sannan ya kuma shaida cewa a halin da ake ciki jam’iyyar APC ita ce a mafita ga ‘yan yankin domin samun hanyoyin cigaba.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Swiss ta dawo wa Najeriya da dala miliyan $370

A don haka ne Alagbada ya sanar da ajiye mukamin shi na mataimakin shugaban majalisar gami da sanya takalmansa ya fice daga jam’iyyar ta PDP

Dama dai tuni wadanda suka fito daga mazabar Ise/Orun masu tunanin za’a tsayar da dan takara daga cikinsu Prince Dayo Adeyeye da Barrister Owoseeni suka yi fatali da hukuncin gwamnan na tsayar da mataimakinsa takarar gwamnan a PDP.

“Saboda haka nima a yau zan yi amfani da wannan damar don sanar da ficewa ta daga PDP zuwa APC”.

Tuna baya jam’iyyar ta PDP ta yi sharin wani dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Ikole 1 Gboyega Aribisogan, wanda shi ma ya shige APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel