Shugaba Buhari ya taya Mahaifin Okonja-Iweala murnar cika shekara 90 a Duniya

Shugaba Buhari ya taya Mahaifin Okonja-Iweala murnar cika shekara 90 a Duniya

Mun samu rahoton cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga Farfesa Chukwuka Okonjo, wanda ya cika shekara 90 a Duniya a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Baya ga shahara a fannin nazarin Lissafi da tattalin arziki, Farfesa Okonjo wanda shine sarkin gargajiya na al'ummar Ogwashiukwu, ya kuma kasance Mahaifi ga tsohuwar Ministar Kudi a ta Najeriya, Dakta Ngozi Okonja-Iweala.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasa Mista Femi Adesina ya gabatar da a madadin shugaba Buhari ya bayyana cewa, yana tarayya tare da al'ummar Ogwashiukwu dake jihar Delta wajen taya murna ga Jagoran su da ya cika shekaru 90 a duniya.

Hakazalika shugaba Buhari ya taya murna ga abokan arziki, na aiki da kuma iyalan Mahaifin tsohuwar Ministar kudi dangane da wannan mataki na rayuwa da wannan fitaccen masani ya taka wanda ke da babbar nasaba a harkar ilimi ta Najeriya.

Mahaifin Okonja-Iweala; Farfesa Chukwuka Okonjo

Mahaifin Okonja-Iweala; Farfesa Chukwuka Okonjo

Shugaban Buhari ya kuma yabawa ingancin jagoranci da ilimi na Okonjo da ya kafa wani babban tarihi cikin kasar nan ta Najeriya sakamakon jajircewa wajen neman ilimi tun yayin samartakar sa.

Shugaban kasar ya hikaito yadda Okonjo ya kammala Digiri din sa na farko a fannin nazarin Lissafi tare da yiwa karatun sa garambawul da digiri na biyu har nau'i biyu a fannin nazarin tattalin arziki da kiyasi inda ya dora da na uku watau digirgir a fannin nazarin lissafi.

KARANTA KUMA: Fasto ya bayar da Gudunmuwar N1m domin Kammala Ginin Masallaci a birnin Calabar

Hakazalika shugaba Buhari ya na da yakini dangane da yadda Mahaifin tsohuwar Ministan ya taka muhimmiyar rawar gani cikin rayuwar malumma tare da tasirin albarka ga ma'abota neman ilimi gami da 'ya'yayen sa da jikoki wanda a yanzu ya zamto wani madubi na rayuwar sa ga kasa baki daya.

Ya kuma yi addu'a ta neman Mai Duka ya kara jan zamanin Sarkin Ogwashiukwu da kuma ingantacciyar lafiya da za ta bashi dama wajen ci gaba da yiwa al'ummar Kasar nan hidima.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel